
Jihar Kano, WHO Da Sauran Masu Bada Tallafi Sun Kaddamar Rigakafin Cutar Polio Ga Yara Miliyan 3.5 A Kano
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
A Kokarin Gwamnatin Kano na sake fatattakar cutar polio daga Jihar Kano, tare da haxin guiwar hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sairan masu bada tallafi daga kungiyoyi sun Kaddamar da gangamin rigakafin cutar polio da ake sa ran yiwa yara Miliyon 3.5 a jihar Kano wanda aka gudanar a Karamar hukumar Dawakin Kudu.
Da yake gabatar da Jawabin maraba shugaban kwamitin rigakafin cutar ta Polio na Jihar Kano wanda kuma shi ne mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana Kyakkyawan fatan da Gwamnatin Kano ke dashi na ganin a kakkabe wannan cuta daga Jihar Kano dama kasa baki daya.
Yace ko da ganin yadda Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya dauki wannan shiri da muhimmancin gaske, kasan Gwamnatin Kano ta kaddamar da wannan shiri ne bil halli da gaskiya, don haka sai ya buqaci jama'a da su bada hadin kan da ake bukata domin samun nasarar shirin.
Da yake gabatar da jawabin sa, Kwamishinan Ma'aikatar lafiya na Jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa Karamar hukumar Dawakin kudu na cikin kananan hukumomin da suka fuskanci matsalar shirin sakamakon yadda karamar hukumar keda garuruwa masu wahalar isa, yace wannan ce tasa aka kawo bikin kaddamar da wannan gangami nan domin karfafatsu wajen rungumar Shirin
Dr. Labaran ya jinjinawa kokarin Gwamna musamman yadda yake baiwa harkokin lafiya Kyakkyawan kulawa sannan ya bukaci jama'a dasu tabbatar da ganin kowa an yiwa yaransu wannan rigakafin domin kawo qarshen cutar ta Polio, Hakazalika ya yabawa Hukumar lafiya ta Duniya da sauran aminan su wajen bada gudunmawar da ake buqata domin ganin wannan shiri ya samu gagarumar nasara.
Gwamnatin Jihar Kano Injiniya Abba Kabir wanda kuma shi ne ya kaddamar da gagangamin rigakafin da aka tsara yiwa yara Miliyon 3.5 ya bayyana cewa Alokacin mu'kin Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne aka samu nasarar kakkabe cutar ta polio baki daga jihar Kano a wancan lokacin, amma saboda rikon sakainar kashin Gwamnatocin da auka gabata aka sake samun bullar cutar a Kano.
Don haka sai Gwamnan ya tabbatar wa da al'ummar Kano cewar duk wani shiri ko tanadi tuni Gwamnati ta gama, yanzu tsunduma aiki kawai za'ayi, don haka sai ya godewa Hukumar Lafiya ta Duniya tare da sauran masu da tallafi bisa irin gudunmawar da suke bayarwa, haka kuma ya bukaci iyaye musamman mata auyi Kokarin kai yaransu domin yi masu allurar rigakafin cutar ta polio.
Daganan ne kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da gangamin inda da kansa ya digawa wasu yaran wannan allurar ta riga-kafi domin muhimmanci ta, sannan ya bukaci jami'an lafiya na jihar Kano dasu rubanya Kokarin da suke domin ganin anyi bankwana da wannan cuta ta polio.
Shima da yake gabatar da jawabinsa Wakilin hukumar Lafiya na qasarnan Dr. Walter Kazadi Mulombo wanda wakilin hukumar WHO anan Jihar Kano Dr. Mayyana Sanusi Abubakar ya wakilta ya bayyana cewa domin tabbatar da ingantaccen shirin aiwatarwa tare da kulawa da qa'idojin SOPs da na Hukumar lafiya ta Duniya WHO wanda suka samar da ma'aikata 484 na sa ka,i da kuma wasu 68 waxanda suka sadaukar da kansu domin gudanar da shirin, Sai kuma 45 a matakin kananan hukumomi, da 19 mataimakan jami'an cibiyoyin lafiya da kuma guda 6 da suke jagorantar domin bayar da goyon dunmawa ta fuskar kwararru.