Wakilin Gaya, Albashi Da Ajingi Ya Kaddamar Da shirin Raba Buhu 18,600 Na Gero Sauran Kayan Abinci Ga Al'ummar Sa



Wakilin Gaya, Albashi Da Ajingi Ya Kaddamar Da shirin Raba Buhu 18,600 Na Gero Sauran Kayan Abinci Ga Al'ummar Sa

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

Wakilin al'ummar Kananan Hukumomin Gaya, Ajingi da albasu a majalisar wakilai ta tarayya, Dakta Ghali Mustapha Tijjani Panda ya kaddamar da rabon buhu 18,600 na Gero da sauran kayan abinci Ga al'ummar mazabarsa

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da rabon a Garin Gaya ranar asabar din nan a harbar cibiyar lura da harkokin addini na Karamar hukumar Gaya. Hon. Panda yace bisa la'akari da halin kalubale da matsin da ake fama dashi na tattalin arziki, ya fahimci ba shida wani zabi da ya wuce raba irin wannan tallafi ga al'ummar yankin da yake wakilta

Ya bayyana shirin nasa na raba buhu 3,600 mai nauyin Kg 25 na shinkafa da buhu 3000 na shinkafa mai nauyin Kg 10. Ya Kara da cewa buhu 6000 mai nauyin Kg 10 na Gero, fulawa buhu 6000 itama mai nauyin Kg 10 da kuma Gero duk za'a rabawa al'ummar yankin nasa.

Panda ya kara da cewa, Tallafin na tare da rabon Naira Miliyon 20 da ake fatan rabawa matasa 1000 na yankin, wannan na cikin tsare tsaren ayyukan mazabar sa na shekara ta 2024.. "A zango na biyu zamu raba kayan Noma ga dubban manoma, inda ya kara da cewa a zango na uku kuma za'a kaddamar da shirin koyawa matasa sana'un dogaro dakai guda 3,000 maza da mata.

"A kashi na 4 zamu gyara tare da gina ajubuwa da hanyoyi.', za muyi abinda ya kamata da dan abinda ke cikin kasafin kudin mu. Inji shi A jawabinsa na godiya Kantoman rikon karamar hukumar Gaya Alhaji Abubakar Jazuli Usman Gaya ya jinjinawa Panda bisa wannan abin alhairi, ya kara da cewa sabbin zubin wakilan al'ummar, musamman na Jam'iyyar NNPP sune mafiya alhairi a tarihin Kano bisa jajircewarsu kan samar da abubuwan alhairi da suke domin kyautata rayuwar al'umma, daga nan sai ya bukaci sauran da suyi koyi dashi.

'Yace wadanda basu kai ga samun kayan abincin ba, ina tabbatar masu da cewa nan bada Jimawa ban nasu rabon zai iso. Za kuyi murmushi domin ina da tabbacin kuna da kyakkyawan wakilci." Kamar yadda Jami'in yada labaran karamar hukumar Gaya Auwalu Musa Yola ya shaidawa manema labarai
I BUILT MY SITE FOR FREE USING