Abdullahi Muhammad Sheka
3 min read
24 Jun
24Jun

Kokarin Tava Kimàr Wakilin Musawa/Matazu Soki Burutsu Ne Tsantsa- 


Daga Abdullahi Muhammad Sheka 


Alokacin da jama"a masu kyakkyawan tunani da fatan alhairi ga Al'umma ke yiwa wakilansu kyakkyawan zato, su kuwa masu fushi da fushin wasu an mayar dasu 'yan mashin ka na jiyo, ta yadda ake amfani dasu wajen yiwa mutane masu kima da Mutunci, wanda wanda qazafi, batanci tare da kagen abinda bashi da tushe balle makama.


Jagoran Qungiyar masu kishin yankin Musawa da Matazu ne ya bayyana haka alokacin da yake yin  martani kan wani batanci da wani ko wasu ke yi kan zargin rashin nagartattun takardun makaranta na wakilin Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu wanda akayi a wata jarida 


Yace wannan surutai sun fi kama da labarin kanzon kurege  wanda wadancan yan aiken keta  fakamniya domin batanci ga wakilin al'ummar Musawa/ Matazu a Majalisar wakilai ta tarayya. Ya zama wajibi ga waxancan mutune da wadanda suke turoso shi da waxanda suka turo su dasu koma makaranta, su tambaya wace shaida ce tafi zama wajibi ga mai bukatar yin takara ya mallaka.


Ya kara da cewa, shaidar  kammala sakandire ce tafi zama wajibi da ake bukata ga duk mai bukatar takara, sannan ya kasancexadan wannan yankin da ya fito ne, sannan ya kai shekara 30 da haihuwa, don haka abinda wadannan  'yan aiken keyi tsananin hassada ce  sannan kuma wani kirkirarren labari ne,  domin wanda ya yi su ya gaza ambatar kodà wuri daya da wakilin Musawa/Matazun ya gaza. Don haka muke kiran wannadannan 'yan aiken su gaggauta janye kalaman nasa ko mu gurfanar dashi gaban kuliya. 


Muna tunawa masu irin wannan hassadar cewa babu wani dan takara da jam'iyyar APC ko kuma kowacce ham'iyya da zaici zabe data tsayar face ta tantance shi. Don haka wannan kalamai tamkar raina hukumar zave ne ga su kansu Jam'iyyun siyasa


Daganan kuma hukumar zabe itama ta gudanar da na tantacewar kafin bashi shaidar shiga takara. Duk an wuce wannan matakan har yaci shekara biyu a majalisar wakilai yanzu suka fahimci bashi da ingantattun takardu? Muna Jan hankalin masu irin wannan qullekulle kullen da iyayen gidansu, su fito fili su daina turo wasu suna amfani dasu wajen batanci ga mutane masu daraja. Ba zai yiwu mu zuba ido qoqakikarin cin zarafin mutanen Kirki.


Wannan soki burutsun bai wuce butulci ba, domin anyi walkiya munga kowa wadanda wannan bawan Allah Hon. Abdullahi Aliyu  ya yiwa sha biyu ta arziki, amma saboda kila sun gabatar da wata bukata da kila ta saba da tsari, rashin samun bukukar tasu tasa suka shiga alyin batanci ga wakilin Musawa da Matazu, kuma muna tabbatar masu lokaci zaiyi da zamu sanar da jama"a  su wane wadannan dake kokarin dakile kyakkyawar aniyar Hon. Abdullahi Aliyu.

Comments
* The email will not be published on the website.
I BUILT MY SITE FOR FREE USING