Kokarin Taba Kimar Wakilin Musawa/Matazu Soki Burutsu Ne Tsantsa-
Daga Abdullahi Muhammad Sheka
Alokacin da jama"a masu kyakkyawan tunani da fatan alhairi ga Al'umma ke yiwa wakilansu kyakkyawan zato, su kuwa masu fushi da fushin wasu an mayar dasu 'yan mashin ka na jiyo, ta yadda ake amfani dasu wajen yiwa mutane masu kima da Mutunci kazafi, batanci tare da kagar abinda bashi da tushe balle makama.
Jagoran kungiyar masu kishin yankin Musawa da Matazu ne ya bayyana haka alokacin da yake yin martani kan wani batanci da wani ko wasu ke yi kan zargin rashin nagartattun takardun makaranta na wakilin Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu wanda akayi a wata jarida
Yace wannan surutai sun fi kama da labarin kanzon kurege wanda wadancan 'yan aiken keta fakamniya domin batanci ga wakilin al'ummar Musawa/ Matazu a Majalisar wakilai ta tarayya. Ya zama wajibi ga wadancan mutune da wadanda suke turo su dasu koma makaranta, domin neman ilimi, sun mai da hankali su san wace shaida ce tafi zama wajibi ga mai bukatar yin takara ya mallaka.
Ya kara da cewa, shaidar kammala sakandire ce tafi zama wajibi da ake bukata ga duk mai bukatar takara, sannan ya kasance dan wannan yankin da ya fito ne, sannan ya kai shekara 30 da haihuwa, don haka abinda wadannan 'yan aiken ke damunsu bai wuce tsananin hassada ce sannan kuma wani kirkirarren labari ne, domin wanda ya yi su ya gaza ambatar kodà wuri daya da wakilin Musawa/Matazun ya gaza. Don haka muke kira ga wadannan 'yan aiken su gaggauta janye kalaman nasu ko mu gurfanar dasu gaban kuliya.
Muna tunawa masu irin wannan hassadar cewa babu wani dan takara da jam'iyyar APC ko kuma kowacce jam'iyya da zaici zabe ta tsayar face ta tantance shi. Don haka wannan kalamai tamkar raina hukumar zabe ne da su kansu Jam'iyyun siyasa
Daganan kuma itama hukumar zabe itama ta gudanar da nata tantacewar kafin bashi shaidar shiga takara. Duk an wuce wannan matakan har yaci shekara biyu a majalisar wakilai yanzu suka fahimci bashi da ingantattun takardu? Muna Jan hankalin masu irin wannan kulle kullen da iyayen gidansu, su fito fili su daina turo wasu suna amfani dasu wajen batanci ga mutane masu daraja. Ba zai yiwu mu zuba ido ana jokarin cin zarafin mutanen Kirki ba.
Wannan soki burutsun bai wuce butulci ba, domin anyi walkiya munga kowa, wadanda wannan bawan Allah Hon. Abdullahi Aliyu ya yiwa sha biyu ta arziki, amma saboda kila sun gabatar da wata bukata da kila ta saba da tsari, rashin samun bukatar suka shiga aikin batanci ga wakilin Musawa da Matazu, kuma muna tabbatar masu lokaci zaiyi da zamu sanar da jama"a su wane wadannan masu kokarin dakile kyakkyawar aniyar Hon. Abdullahi Aliyu.