Sakamakon Matsalar Rashin Ruwa, Muryar Jama"ar Sheka Ta Gyara Rijiyar Burtsatsen Primary Sheka
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
A Kokarin da ta ke na ganin an samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a makarantun Sheka, Kungiyar Muyar Jama"ar Sheka Ta gudanar da aikin gyaran Rijiyar urtsatsen Makarantar sheka Peomary wadda ta jima alalace.
Jawwbin haka ya fito ta bakin shugaban kungiyar Muryar Jama"ar Sheka Servy. Malandi Umar Kura cikin wata sanarwa da jami'in yada labarn kungiyar Abdullahi Muhammad Sheka ya rattabawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano cikin wannan makon.
Servy Malandi yace bayan ziyarar da kungiyar ta kai makarantar ta Sheka primary, "Mun samu korafin matsalar ruwa wanda lalacewar rijiyoyin dake makarantar suka yi, nan ta ke shugaban ya bada unarnin kirawo masu gyara kuma alhamsulillahi gashi yanzu har an kammala gyara ruwa ya samu a makarantar. Inji Servy Malandi
Hakazalika shugaban kungiyar ya bayyana cewa ba makarantar Sheka primary kadai zata amfana da manufofin wannan kungiya ba domin wannan kungiya ta ziyarci asibitin sheka da makarantar 'Yan mata ta shska wadda suke fama da barazanar ambaliyar ruwa, kuma tuni kungiyar ta turo masana harkokin fasalin kasa inda suka gudanar da gwaje gwaje kuma yanzu haka muna sauraron rabotoninsu domin yin nazarin
sa tare da duba irin aikin da za'a yiwa wuraren biyu.
Malandi Kura ya kuma sanar da aikin zagayen unguwanni shida dake Sheka inda a halin yanzu aka ziyarci hudu daga ciki kuma akan tattauna matsalolin dake damun kowacce unguwa da kuma irin nasarorin da kungiyoyin unguwannin suka samu a yanayin ayyukansu.
A karshe Malandi Kura ya bayyana cewa duk abinda wannan kungiya ta Muryar Jama"ar Sheka zata yi na bakin dayan sheka zata yi, domin ita Shekar take kallo baki daya, saboda haka ya bada umarnin cewa kowacce kungiya ta ci gaba da aikin ta kamar yadda ta saba.