1 min read
14 Jul
14Jul

Muna Mika Sakon Ta'aziyyar Mu Bisa Rasuwar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano 

A madadin hadaddiyar kungiyar 'yan Kasuwar  Jihar Kano, shugaban kungiyar Alhaji Auwalu Gabari Jakada na gabatar da sakon ta'aziyya a madadin 'Yan Kasuwar Kano ga iyalai, Gwamnatin Katsina da Kasa baki daya bisa wannan babban rashi.

Alhaji Auwalu Gabari Jakada ya bayyana wannan sako kamar yadda mai magana da yawun shugaban Abdullahi Muhammad Sheka ya rattabawa rattabawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ci gaba cewa Tsohon Shugaban Kasar Muhammadu  Buhari ya hidimtawa kasa a matsayin soja wanda har takai ya Shugabancin Kasa alokacin Mulkin Soja kafin yin ritayarsa, sannan kuma aka zabe shi a matsayin Shugaban Qasa na mulkin farar hula wanda ya kwashe Shekaru takwas yana hidimtawa kasa.

Daga nan Sai Alhaji Auwalu Gabari Jakada ya yi addu'ar fatan Allah ya kyautata makwancinsa yasa aljannatul Firdausi ce makomar sa, sannan ya kara addu'ar Allah ya baiwa iyalansa jure wannan babban rashi.

Comments
* The email will not be published on the website.
I BUILT MY SITE FOR FREE USING