Shekara 76 Masu Albarka Na Dr. Abdullahi Umar Ganduje Sai Godiya-Prof Sabo
A Madadin Ni kaina, iyalai na, Al'ummar Karamar Hukumar Bichi da Kuma Jagoran mu Masoyin jama'a Rt. Hon Abubakar Kabir Abubakar Muna Mika sakon Taya Murnar cika Shekaru 76 Masu albarka na Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam)
Babu Shakka Al'ummar Karamar Hukumar Bichi na alfahari da wadannan Shekaru masu Albarka, musamman batun ingantaccen Jagoranci, kyakkyawar tarbiyyar addini da Kuma kishin Kano da Kanawa.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ka tabbata Abin koyi, sannan zamu Ci gaba da biyayya tare da yi maka addu'ar Fatan Karin shekaru masu Albarka.
Allah ya kara lafiya da nisan Kwana, ya karawa rayuwar albarka, Mu da Jama'ar Bichi karkashin jagoranmu Rt. Hon. Abubakar Kabir Abubakar Muna Mika wannan sako sannan Muna Kara jadadda mubayi'armu ga wannan tafiya mai tarin Albarka.
Mun gode kwarai da gaske
Prof. Muhammad Sabo