3 min read
06 Jun
06Jun

AN QADDAMAR DA KUNGIYAR MURYAR JAMA"AR SHEKA Don Magance Matsalolin Tsaro

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano


Rana ta Lahadin data gabata aka gudanar bikin qaddamar da qungiyar Muryar Jama"ar Sheka domin tunkarar matsalolin faxace faxacen daba, kwancen waya da mummunar matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi wadda ke zaman wani babban valuable da a kullum ke vata sunan garin na Sheka


Da yake gabatar da jawabinsa, Dagacin Sheka Alhaji Abubakar Musa Zakari wanda kuma shi ne mai masaukin baqi ya bayyana dalilqn kafa wannan babbar qungiya wadda yace zata aiki kafaxa da kafaxa da sauran jami'an tsaro domin magance matsalolin faxace faxacen da da sauran nau'ikan laifuka dake barazana ga xorewar zaman lafiyar yankin baki xaya.

Dagacin ya bayyana cewa akwai kyakkyawan fatan da akewa wannan qungiya musamman ifan aka calling sunshine ahugabannin da zasu jagoranci qungiyar. Ya kuma buqaci kowa da kowa ya taro domin sauya kallon da akewa wannan gari mai albarka, inda ya buqaci haxin kai da goyon bayan kafafen yaxa labarai domin ganin an gudu tare kuma an tsira tare.


Da yake gabatar da nasa jawabibsa bayan qaddakar da qungiyar Muryar Jama"ar Sheka  shugaban Qungiyar sevy. Maland Umar Kura ya bayyana aniyarsu nayin aiki tiqieu domin ganin basu baiwa al'ummar sheka kunya ba kan lyakkyzaton da alayi masu har aka aminta da xora masu wannan nauyi. Don haka ya ce Muryar Jama"ar Sheka zata zama wata murya da zata Ci gaba da tattaunawa da sauran makwabtan unguwanni dake zagaye da ita domin samar da tabbataccen zaman lafiya


Hakimin Gundumar Mariri  Amb. Jarman Kano ya bayyana farin cikinsa bisa kafa wannan qungiya wanda yace wannan qoqari na cikin aniyar Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wanda ya buqaci dagatai da sauran masu riqe saraitu daban daban da su Ci gaba da bujiro da abubuwan da zasu taimaki al'umma,  Don haka sai ya buqaci sauran Dagatai da suyi koyi da qoqarin Dagacin Sheka kan irin wannan abin alhairi.


Shima anasa jawabin shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Hon Ghali Abdullahi Basaf ya bayyana farin cikinsa da kafa wannan qungiya ta Muryar Jama"ar Sheka, inda ya bayyana maxin ran da yake ji 8dan aka alaqanta garin na sheka da wasu miyagun laifuka, saboda haka sai ya tabbatar da samun haxin kan Qaramar hukuma, sannanbya buqaci jawo matasa a jika domin fahimtar dasu illolin miyagun halaye.


Cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai shugaban qaramar Hukumar Kumbotso, Hon Ghali Abdullahi Basaf, Hakimin Gundumar Mariri, Shugaban Rundunar tsaro ta Vigilanti na Jihar Kano,  MDLEA, Police, Hisba, DSS da Kungiyar Mafarauta.

Comments
* The email will not be published on the website.
I BUILT MY SITE FOR FREE USING